‘Yan sandan Royal Canadian Mounted Police (RCMP) na kasar Canada sun tabbatar da mutuwar mutane 10, ciki har da wanda ake zargin shi ne maharbin, sakamakon wani mummunan harbe-harbe da ya faru a makarantar sakandare ta Tumbler Ridge Secondary School da ke lardin British Columbia.
A wata sanarwa da RCMP ta fitar jiya Talata, ta ce an gano gawar mutane shida a cikin makarantar, yayin da wani mutum ya rasu a hanyarsa ta zuwa asibiti.
Haka kuma, an gano gawar wasu mutane biyu a wani gida da ‘yan sanda ke zargin yana da alaka da harin.
RCMP ta bayyana cewa lamarin ya shafi “mai harbi a makarantar sakandare,” inda aka gano wani mutum da ake kyautata zaton shi ne maharbin ya mutu da abin da ake ganin raunin da ya jikkata kansa da kansa.
‘Yan sanda sun kara da cewa an dauki mutane biyu ta jirgin sama zuwa asibiti sakamakon munanan raunuka masu barazana ga rayuwa, yayin da kusan mutane 25 ake duba lafiyarsu a cibiyar kiwon lafiya ta yankin saboda raunuka marasa tsanani.
An kwashe duk sauran dalibai da ma’aikatan makarantar cikin tsaro, yayin da ‘yan sanda ke aiki tare da hukumomin makarantar domin tabbatar da haduwar iyalai da ‘ya’yansu cikin tsari.
Garın Tumbler Ridge na a gindin tsaunukan Rocky Mountains na British Columbia, sama da kilomita 1,100 arewa da birnin Vancouver, kuma yawan jama’arsa bai wuce 3,000 ba.
Kafafen yada labaran Canada sun rawaito cewa maharbin mace ce, amma RCMP ta ki bayar da cikakken bayani kan wanda ake zargi a wannan lokaci.
‘Yan sanda na ci gaba da binciken wasu gidaje da kadarori a yankin domin gano ko akwai wasu wurare da ke da alaka da harin.
Kwamandan RCMP na yankin arewa, Ken Floyd, ya bayyana lamarin a matsayin “mai saurin sauyawa kuma mai rikitarwa,” yana mai cewa rana ce mai matukar wahala da radadi ga al’ummar yankin.
Firaministan British Columbia, David Eby, ya bayyana harin a matsayin “babbar masifa da ba za a iya misaltawa ba,” yana mai alkawarin cewa gwamnati za ta bayar da dukkan tallafin da ake bukata ga al’ummar Tumbler Ridge a kwanaki masu zuwa.
Duk da tsauraran dokokin mallakar makamai a Canada idan aka kwatanta da Amurka, hare-haren bindiga da suka faru a ‘yan shekarun baya sun kara jawo kira da a kara tsaurara dokokin sarrafa makamai.
Tags
Labarai
