Gwamnan Jihar Adamawa, Ahmadu Umaru Fintiri, ya bayyana dalilan da suka sa ya fice daga jam’iyyar PDP zuwa APC, yana mai cewa matakin ya samo asali ne daga bukatar yi wa al’ummar jihar hidima yadda ya dace da kuma tabbatar da ci gaba mai dorewa.
Gwamnan ya ce bayan dogon nazari da tuntuba da masu ruwa da tsaki, ya fahimci cewa sauyin jam’iyya zai ba shi damar aiki tare da gwamnatin tarayya yadda ya fi dacewa, domin hanzarta aiwatar da manyan ayyukan raya kasa a Adamawa State.
A cewarsa, matsalolin cikin gida da rikice-rikicen shugabanci da suka dabaibaye PDP sun rage wa jam’iyyar karfin tafiyar da manufofi yadda ya kamata, lamarin da ya sa ya yanke shawarar neman dandalin siyasa da zai fi bai wa jihar dama ta ci gaba.
Gwamna Fintiri ya jaddada cewa sauyin jam’iyyar ba wai saboda son zuciya ba ne, illa saboda muradin jama’a, yana mai alkawarin ci gaba da aiwatar da manufofin da za su inganta rayuwar al’umma ba tare da la’akari da bambancin siyasa ba.
Ya kuma bukaci magoya bayansa da daukacin al’ummar jihar da su fahimci matakin, tare da ba shi hadin kai domin cimma burin zaman lafiya, ci gaba da walwala a Adamawa.
Tags
Labarai
