Manyan ƙasashen Turai guda biyar—Birtaniya da Faransa da Jamus da Sweden da Netherlands sun bayyana cewa sun gamsu da hujjoji da ke nuna cewa Rasha na da hannu a mutuwar fitaccen ɗan adawar siyasar Rasha, Alexei Navalny.
A cewar sanarwar haɗin gwiwa da waɗannan ƙasashe suka fitar, binciken dakin gwaje-gwaje da aka gudanar kan samfurin jikin Navalny ya gano wani guba mai matuƙar hatsari da ake cewa ta samo asali ne daga kwayar guba ta kwado (poison dart frog), wacce ba ta samuwa a Rasha.
Hakan, a cewar ƙasashen Turai, ya ƙara ƙarfafa zargin cewa an yi amfani da wannan guba ne da gangan.
Rahoton ya bayyana cewa irin wannan sinadari na guba ba ya samuwa a yanayi na yau da kullum, kuma ana buƙatar ƙwarewa ta musamman da damar fasaha kafin a iya amfani da shi.
Saboda haka, ƙasashen sun ce ba su ga wata hujjar da ke wanke gwamnatin Rasha ba, ganin cewa tana da iko da dama da kuma dalilin aikata hakan.
Sai dai gwamnatin Rasha ta musanta zargin, tana mai cewa wannan batu ƙage ne da farfaganda ta siyasa, tare da jaddada cewa babu wata hujja mai ƙarfi da ke danganta ta da mutuwar Navalny.
Alexei Navalny, wanda ya shahara wajen sukar manufofin gwamatin Rasha, ya rasu ne a wani gidan yari a watan Fabrairun 2024, lamarin da ya jawo cece-kuce a duniya tare da ƙara tsamin dangantaka tsakanin Rasha da ƙasashen Yamma.
Masu sa ido kan harkokin siyasa na ganin cewa wannan sabon zargi na iya haifar da ƙarin takunkumi da matsin lamba na diplomasiyya a kan Rasha a makonni masu zuwa.
Tags
Labarai
