Ambaliyar Ruwa Ta Halaka Mutane 18 A Colombia, Ya Yin Da Dubban Mutane Suka Rasa Matsugunansu.
Kasar Colombia na fuskantar babbar masifa bayan ambaliyar ruwa ta yi sanadiyar mutuwar mutane 18, yayin da dubban iyalai suka rasa gidajensu a arewacin ƙasar.
Jihar Córdoba ta fi sauran wurare munin bala’in, inda ruwa ya malale gidaje da filayen noma da filayen kiwo.
Hukumar agajin iftila'i ta kasar, ta ce fiye da gidaje 4,300 sun lalace, kuma shanu 1,200 sun mutu, abin da ke kawo babban asarar tattalin arziki ga manoma da masu kiwo.
Gwamnatin ƙasar ta bayyana cewa ambaliyar ta shafi mazauna sama da 150,000 a Córdoba kaɗai, yayin da wasu yankuna na arewacin ƙasar ma ke fama da ruwa mai yawa. Hukumar agajin iftila'i ta ruwaito mutuwar mutane 22 da farko, amma daga baya adadin ya sauka zuwa 18.
Domin dakile mummunar tasirin iftila'in, Shugaban ƙasar, Gustavo Petro ya ayyana dokar ta baci na tsawon kwanaki 30, wanda zai ba shi damar daukar matakai na musamman da rarraba kayan agaji ba tare da jiran amincewar majalisar dokoki ba.
Masu sharhi na bayyana cewa iftila'in ambaliyar zai iya janyo tasirin tattalin arziki da tsaro a fannin noma da kiwo, yayin da hukumomi ke kokarin tallafa wa iyalai da suka rasa muhallinsu.
Tags
Labarai
