'Yan ta'adda sun kashe mutane shida tare da tilastawa mutane barin gidajensu domin neman tsira a jihar Sokoto.
Akalla mutane shida ne aka kashe a kauyen Baidi da ke cikin karamar hukumar Tangaza a jihar Sokoto a daren Laraba yayin wani hari da wasu da ake kyautata zaton suna da alaka da kungiyar Lakurawa, wata kungiya mai dauke da makamai a yankin.
Tangaza dai na daya daga cikin yankunan da Amurka ta kai hari a watan Disambar bara a jihar Sokoto.
Yanki ne da ake kyautata zaton ‘yan ta’adda na amfani da shi a matsayin maboya wanda ke kan iyakar Najeriya da da Jumhuriyar Nijar.
Tags
Labarai
