Sojoji sun lalata wuraren jinya na 'yan ta'addan daji, tare da kashe mutum daya a hare-haren da suka Kai jihar Sokoto.
Dakarun rundunar hadin gwiwa ta Operation FANSAN YAMMA reshen Arewa maso Yamma sun fatattaki ‘yan ta’adda tare da lalata wata cibiyar kiwon lafiya da ke asirce a wani farmakin hadin gwiwa da suka kai a tsakanin ranar 21 zuwa 22 ga watan Janairu.
An bayyana hakan ne a cikin wata sanarwa mai dauke da sa hannun jami’in yada labarai na rundunar hadin gwiwar, Captain David Adewusi, kuma aka buga a shafin sada zumunta, X na rundunar sojojin Najeriya da yammacin jiya Alhamis.
Sanarwar ta ce, dakarun runduna ta 8 na Garrison Strike Force da ke aiki tare da ma’aikatar harkokin wajen kasar sun gudanar da wani samame na yaki da 'yan ta'adda a jihar Sokoto, inda suka kashe dan ta’adda guda daya yayin da wasu suka gudu da raunukan harbin bindiga a jikinsu.
Download and Install this App (89MB)
Install from Google Play
Category | Education App |
Developer | Annahda |
Last Update | 23 January, 2026 |
Version Requirement | Minimum 7.0+ |
Application Version | 1.0.3 |
Application Size | 89MB |
Tags
Labarai
