Allah yayi wa fitaccen tauraron Fina-finan Indiya Dhamendra Rasuwa yana da Shekaru 89 a duniya. ya rasu ne a wani asibiti dake birnin Munbai babban birnin Maharashtra na kasar Indiya.
An dai haifi tsohon tauraron ne a Shekarun 1935, 8 ga watan Disamba, kwanaki 14 kenan ya rage ya cika Shekaru 90 a duniya.
Dhamendra ya kasance daya daga cikin manya-manyan jaruman fina-finan Indiya mafi shahara a tarihi inda ya fito a fina-finai sama da 300.
Ya rasu ya bar 'ya'ya 6 ciki har da fitattun jaruman Fina-finai Indiya Sunny da Bobby da Esha.
Tuni dai manya-manyan Jarumai a masana'antar fina-finan na Indiya suka fara mika sakonnin taaziyarsu ga iyalan mamacin.
%20(7)_1.jpeg)
0 Comments:
Post a Comment